Cikakken Bayani Akan Muhawara Tsakanin SOLANA VS ETHEREUM Wanda Fitaccen Masanin Crypto Na Africa Yayi, Wato Sunusi Danjuma Ali. Wannan Rubutun Yanada Mahimmanci Sosai, Zaku Iya Turawa Yan Uwanku Don Su Amfana.
SOLANA VS ETHEREUM
Yan kwanakin nan anata sa toka sa katsi tsakanin mutanen da suka aminta da Solana blockchain da kuma wayanda suke nuna matukar biyayya ga Ethereum blockchain.
Banso cewa komai ba, amma alkalamina chikin dangwalo mini tawada yake domin ganin na rubuta wani abu, yayin da lokachi guda kuma hankada zuchi (emotion) yake karfafar zuchiyata cewa ya kamata nace wani abu akai, tunda inada abin fada.
TECHNOLOGY:
Idan ana maganar karfin tech tsakanin blockchains, Ethereum bashida tsara ayanzu ta kowacce fuskar da take tabbatar da tsayuwa tareda karfin blockchain. Decentralisation, security da scalability dukkansu Ethereum bashida tsara aduk blockchains da muke dasu.
Ko a baya da Ethereum yake fuskantar qalubale wajen scalability, lokachin yana kan tsarin Proof of Work (PoW) consensus mechanism ne, komarsa kan tsarin Proof of Stake (PoS) ya rage gani-gani da ake masa ta wannan bangaren, sannanga Layer two (L2) blockchainsda suke kara taimaka masa ta wannan bangaren.
Kasancewar Bitcoin blockchain amatsayin uba na dukkanin blockchains (father of blockchains), bazai hana a kira Ethereum blockchain cewa shine jagoran dukkan blockchains da ake dasu a yanzu. Domin kuwa har yanzu babu wani blockchain da yazo da sabon abu sabanin wanda Ethereum yazo dashi ba na smart contract wanda babushi kafin zuwansa.
Mafi yawan blockchains da sukazo bayan samuwar Ethereum suna kokarin kwaikwayonsa ne, sai kuma qalilan daga chikinsu da suke kokarin habbaka tsarin da yazo dashi (improvements). Har yanzu babu wani blockchain daya kamo hanyar yawan protocols da suke kan Ethereum blockchain.
Tabbas kasancewa blockchain open source, shine ya zama silar samar da wasu blockchains din bayan Ethereum, da ace blockchain close source ne da mafi yawan blockchains ba’a samar dasu ba. A bangaren tech, a yanzu Ethereum bashida sa’a ko tsara.
CRYPTOCURRENCIES:
Mutanen da sukafi ta’ammali da cryptocurrencies sun rabu kaso biyu, wato traders da/ko holders. Tuna hakan zai saukakawa mutanen da suke dambarwa akan Solana blockchain da Ethereum blockchain. Traders basa kallon inganchi ko rashin inganchin projects da tokens dinsu, shine ma yasa tsarin binchikensu akan token kawai yake tsayawa (technical analysis) ba ruwansu da project dinsa.
Shifa trader koda an bashi tabbachin token zai mutum nan da awa daya (1hr), indai zai bashi riba chikin minti hamsin (50′) kafin ya mutu, zai saka masa kudi yachi riba dashi chikin wannan 50′ din, idan yaso bayan 10′ token din ya mutu . Holders sune suke damuwa da kyawun project (use case) da utilities da suke kan token (fundamental analysis), domin lissafinsu akan token bana kusa-kusa bane, lissafine mai dogon zango, don haka dole su kiyaye tareda taka tsan-tsan wajen sawa token kudi.
Fahimtar wannan zai saukakawa mutane banbanchin tokens da ake kirkirarsu akan Solana blockchain da tokens da ake kirkirarsu akan. Mafi akasarin tokens da ake kirkirarsu akan Solana blockchain (>90%) meme tokens ne masu bads riba sosai chikin kankanin lokachi, amma kuma sunada hatsarin gaske ga traders.
Da yawan Solana blockchain meme tokens basa fin awanni ko yan kwanaki ake chin kasuwarsu suke watsewa su mutu murus, sai qalilan daga chikinsu wayanda suke haura kwanaki, wasuma har suyi watanni ana damawa dasu. Mafi yawan projects da tokens dinau da ake kirkira akan Ethereum blockchain zaka samu yan gaske ne, masu projects ko tokens din ba yan chin dare daya kumburin chiki bane irin na Solana.
READ: All About Blockchain Technology: Origin, Core Features, Advantages & Types
Tokens na kan Solana blockchain sunfi saurin ninnikawa traders kudin su (Xs), musamman duba da cewa akan Dex ake trading dinsu. Sabanin tokens na kan Solana, tokens na kan Ethereum basu fiya yiwa traders koda 1X ba, a mafi yawan lokachi saidai suba da ribar percentage (ROI) na kudin da aka saka musu (initial investment). A trading na Solana tokens, chikin sauki ake rugpulling traders, a gudar musu da kudi, abarsu da tarin lambobi marasa amfani a wallet. Hakan bai fiya faruwa a tokens da suke kan Ethereum blockchain ba (koda kuwa meme tokens dinsa ne).
Wanda ya iya playing Solana na degen trading well akan Solana, ba abinda zaka fada masa domin gamsar dashi akan ya daina, bazai yiwu ba. Hasalima mafi yawan wayanda suke degen trading akan Solana yanzu, kallon masuyi trading a CEX wahalallu suke, domin masu trading a CEX sai suyi kwanaki akan token, daya basu ribar 20% sai suyi murna, yayin da mai Solana degen yakan iya samun X10 chikin yan awanni. Idan muka duba masu sayen token domin holding, zamuga sunfi karkata kan token na kan Ethereum, saboda sunfi tabbas da samarda nutsuwa azukatan masu siyansu.
Farashin $SOL a Mahangata:
$SOL yayi mummunar faduwa har zuwa $8 bayan yakai ATH dinsa na $259 a last bullrun, lokachin daya samu hype na kirarin Ethereum killer. Kwatsam! sai Solana blockchain suka bijiro da dabarar fara kirkirar meme tokens, sannan chikin sa’a sai trend ya bisu, wanda zamu iya cewa sune babban utility daya jawo tashin farashin $SOL ayanzu. Hakan ya jawo bukatar $SOL sosai domin shiga degen trading ga miliyoyin traders, wannan ya jawo dagawar farashin $SOL har zuwa $210 a baya-bayan nan.
Kenan zamu iya cewa farashin $SOL a yanzu ya ta’allakane ga meme tokens da ake kirkirar masa, da kuma karbuwarsu ga degen traders. Su kuma meme tokens da degen traders yayin blockchain suke (trend). Irin wannan trend din da Solana yake yi a yanzu na meme tokens, irin sane ya daga shuhurar BSC blockchain da dagawar farashin $BNB daga kasa da $40 zuwa $690 a last bullrun. Yawan bukatar $BNB domin trading na meme tokens (shitcoins a wancan lokachin) shine ya kawo hauhawar farashinsa zuwa ATH dinsa.
Yanzu da trend yabar kan BSC blockchain, me kuke tunanin zai faru da farashin $BNB da ace Binance da BSC basu fito da wasu dabaru (strategies) da zasu rike farashin sa ba? Ya kuke ganin farashin $BNB zai kasance da ace ya dogarane kawai da iya bukatuwarsa domin trading shitcoins a DEX ba?
A yanzu zamu iya cewa farashin $SOL ya godarane dabukatuwar $SOL din domin trading meme tokens dinsa. Me kuke tunanin zai faru da farashin $SOL idan trend yabar kansa? Musamman duba da cewa Base blockchain ya fara shura, da kuma alamar watakila shine zai maye gurbin Solana a bangaren trading na meme tokens, kamar yanda Solana ya kwace trend daga kana Arbitrum blockchain, har yayi karfi irin nan BSC abaya.
About SUNUSI DANJUMA ALI
Sunusi Danjuma Ali is a Youtuber, Content Creator/Writer, Community Moderator, Social Media Branding, and Influencer in Cryptocurrencies and related financial initiatives. || Crypto Content Creator || Founder: @SCTv Africa